mijinki ko mijina page 1

*MIJINKI KO MIJINA*
{NWA}
NA B ALEEYU
Page 1
Sauri yake sosai yaje gurin tilon 'yarshi da baisan wani hali take cikiba zuciyar Shi cike da fargabar abunda zai tarar, sallama yayi tareda neman izini aka basa damar shiga gidan, kansa ak'asa har ya wuce k'ofofin mak'otan Shi, "a'a baban banuja andawo sannu da zuwa ya kasuwa "
"Kasuwa lafiya Lau Alhamdulillah" yabata amsa tareda ciro alawa a aljihun rigarshi yace gana atika batareda ya kalle ta ba, "Kai dai baban banuja baka rabuwa da đawainiya toh anagode sosai Allah yasaka da alkhairi yak'area buđi Allah yajik'an maman banuja"
"Ameen Ameen"idon Shi tab da hawaye yawuce đakin Shi. A hankali yatura kofar đakin yasa meta kwance kan tsohuwar katifar su tana wasa da k'afafunta da alama tayi kuka Har ta gaji, hawaye suka zubo masa ya sunkuceta yana mata wasa, take tafara dariya irin tasu ta jariran da basu wuce wata shida ba, Zaunar da ita yayi cikin k'afafun Shi yana bata kunu Wanda ba siga aciki se madara, tas ta shanye kunun har tana kamo robar.Ruwa yadauko acikin gora ya ya tsiyaya a cup yabata sosai tasha ruwan sannan ya đora ta kan kafadarshi yana yawo da ita ađakin tuni bacci yayi a won gaba da ita ajiyar zuciya yayi yasauketa kan katifar su yamata rufa da bargo tareda tofeta da addu'a
Bayi ya shiga yafito a hanyar Shi ta fitowa ya hadu da talatu, sama da kasa take kallon shi Sannan ta buga mishi tsaki "an daiji kunya wlh rayuwa bata an fanu Mai ita ba " kallonta yayi kurum yace "Allah yashiryadda ke" ya juya warshi yazo kan dakalin dakin shi yana Al'wala "Kace Allah yashir yani kaima Allah ya shiryadda kai daga wannan bakar rayuwa daka daukarwa kanka, ace mutun ba Aure ba dangi sedai yashigo ma mutane gida yana kallon hamatan matan mutane"
Wakkala ce tafito tana tambayar lafiya keda Waye? Talatu tace " nida wannan jarrababben mana " tsaki wakkala tayi kema bakida aikinyi ne dakika tsaya Kula wannan mutun
Dai-dai nan yagama al'wala ya đaga kai sama tareda fađan ( Ashhadu an la'ilaha illallah wa'ash hadu anna Muhammadan rasulillah ) ( Allahummag firli wali walidayya wali man dahala baitil muminun Ameen ) yajuya yajawo đakin Shi yawuce masallaci bakinshi da azkar đin shiga masallaci har ya Kai kofar masallacin yana Addu'a, Bayan anfito daga masallaci suka hadu da mak'otownship gindin iccen mangwaro inda suke shimfida tabarma Dan yada zango, Assalamu Alaikum ya musu sallama, Amin wa'alaikas salam, malam "bubakar ne sannu da zuwa " yauwa Sannun ku nasame ku lafiya? Gaba dai suka amsa masa da lafiya Lau ya fatima? Murmushi yayi Fatima tana gida bacci take, Toh madallah Alhamdulillah"
"Bismillah suka fara cin tuwon gidan malam kabiru Sannan aka ci na gidan yusha'u Dana sauran lokacin Da aka zo cin na gidan nuru Mai kafinta dak'yar malam bubakar yake cin abincin saboda k'yank'yamin ta dayake ga Kuma rashin iya abinci kadan yaci yace "Alhamdulillah "
Haka suka watse aka shiga masallacin isha'I suna fitowa aka sake zazzaunawa yafara basu karatu kowanne Dana Shi littafin bayan yagama ya d'ora da tunatarwa yayi musu nasiha sosai akan saninsa yabada umurni inda mai tambaya babu yarufe da addu'a yamusu seda safe, yashige gidan kamar yanda yasaba sallama da Kuma neman izini, maryama maman atika itace farko Dama kuwa Banda ita Babu Mai Kula Shi agidan koda yayi sallama, wannan Karon ma itace ta karb'i sallamar sukayi seda safe,
🍀🍀 🍀🍀
*MIJINKI KO MIJINA*
NA B ALEEYU
Page 2
Da sallama yashiga đakin yasameta har lokacin tana bacci yayi hamdala yajawo littafan Shi yana dubawa har kusan 12 sannan ya ajiye karatun, ya đaga banuja sama yasa mata nabkin ya maida ta kan katifa shima ya kwanta, cikin dare yaji sautin kukanta yatashi dasauri yajawo mata fidar kununta yabata tasha sosai Sannan ta koma bacci haka yake fama da ita kafun wayewar gari tana tashi shan kunu biyar ko ince shan nono
Kiran farko na asubah yatashi yayi al'wala yawuce masallacin asubah a kofar fitarshi suka hade da sauran 'yan gidan tareda mak'otanshi su biyar cib sukayiwa Juna Ina kwana tareda shigewa cikin masallacin, seda gari yawaye yashigo gidan, cike da murnar bai same kowa ba yashige đakin shi dasauri dayake jiyo kukan banuja tun kofar gidan Amma babu Wanda yayi hankalin shiga đakin yadauko ta bare ya rarrasheta, Dama maryama ce ke Kula da ita itakuma hidimar nata 'yayan take Sekuma idan batajiba kasancewar đakin ta shine farkon shigowa gidan
Risho ya kunna yadora ruwan zafi yayi mata wanka yacanza mata kaya Sannan yakai nafkin d'inta shara goya ta yayi yashiga gyra đakin tsab yagama ya kunna tiraren tsintsiya, sallama akayi yace "shigo" Nasiru ne đan maryama yace sannu "Baba Ina kwana "
" lafiya Lau nasiru katashi lafiya ya sauran k'annen ka?
"Lafiya Lau baba Dama ummana ce tace inzo in diba ya kwanan banuja da Abban ta " baban banuja yayi murmushi "gata nan harta koma bacci "
Leda ya mik'a mishi "gashi inji babana" Babban banuj yace "Toh kudai bakwa gajiya da Abun alkhairi Toh kace angode ungo alawa kuje makaranta Banda nakara fah " yaron ya karba yana washe hakora yana fita sauran yaran suka fara shigowa suna baban banuja Ina kwana, ya d'auko alawar ya raba musu Kowa đađđaya suka wuce suna murna, haka yake kullum dasafe zai rabawa yara alawa suje makaranta idan yadawo da yamma zai raba musu inibi wato (dabino) baban banuja kenan mai kyauta da k'ari mai hakuri da tawakkali
Karfe goma na safe yafito bayan yayi wanka yashir ya zai wuce shagon Shi na ni'kar gari da kullu, maryama ta karbi banuja kasancewar tana yarda da ita, haka Zata hađasu da atika wadda banuja tabawa kwana arba'in tayi ta renon su kafun baban banuja yadawo da amincewar malam kabiru mijinta, dayake tin zuwansa gidan baban banuja shine mutun na farko daya taimaka masa matarsa Kuma margayiya hadiza Itama ta taimaki matarshi maryama kasancewar maryama tayi ciyo sosai har ancire rai, wannan hađin kan nasu yajawo musu k'iyayya mai karfi tsakanin su da matar nuru kafinta da kuma matar iro mai nama, sosai suke k'in hadiza ganin mijinta yafi nasu wadata ko da rana đaya bata taba saka musu da sharri ba sedai tabisu da alkhairi, wannan kenan
Tabarma ta shimfida musu ta Dora katifa akai Sannan taje ta dama musu custard da madara ta jawo banuja dake k'ok'arin done kanta k'asa ta fara bata ganin haka yasa atika rarrafowa tana kuka tas tagama bawa banuja ta goge mata jikinta sannan tajawo 'yarta atika tabata, wakkala ce tayi tsaki "andaiyi asarar rayuwa wlh kace d'an wani yafi naka wanin ma matacce"
maryama ta rantse ido tana jin zafin duk lokacin Da zasu dab'awa margayiya hadiza magana har cikin ranta take jin zafin hakan, talatu ta karbe zancen da cewa "waya sani ko suna sakayawa da uban 'yar "
"Ke talatu maryama ta Mike tsaye tana nunata da yatsa Bari ganin Ina samuku ido duk Abunda kukayi Toh wlh kisani ba tsoron ku nake jiba Ina raga muku ne Dan kunfi k'arfin shekaruna Amma tunda hakan kuke so muzuba Dan halak ka fasa"
Muryar mijinta taji malam kabiru a đaki yana cewa "kin zubadda sauran ragowar da kike ik'irarin kina musu shin ban gaya miki ko dukan ki sukayi ba ki zuba musu ido "
"Duka ta maimaita zancen anzo gun wlh angzo gun da har kake tunanin mace zata dakeni a zauna lafiya wadda bata kai sa'annin haihuwa taba"
"Shikenan maryama wuyanki yakai Ina fada kina fada a gaban yaranki " atake jikin ta yayi sanyi ta kwashe yaran ta shige cikin d'akin dasu " Dan Allah kayi hakuri idan ranka ya baci wlh sun isheni mutanen nan Kaji mummanan kalamin da suka jefeni da Shi "
" Ina jin duk Abunda kuke Amma bai kamata kibiyewa karnai irin su ba domin basuda maraba da karnai.
🍀🍀 🍀🍀
*MIJINKI KO MIJINA*
NA B ALEEYU
page 3
Da yamma yashigo gidan bayan yara bawa yara inibi suka watse suna murna, a goye yasamu banuja kan bayan nasiru yayi murmushin jin dadi "agaida nasiru Allah ya maka albarka " ya karb'i banuja tana Ganin shine tafara ihun su na yara tana murna d'akin Shi yashige da ita ya Dora ta kan kafadarshi yana mata wasa harta soma kuka ya Han kad'a rigarta yaga cikinta ya lafe yasoma hada mata kunu da madara wanda babu sugar aciki dasauri takama k'aramun kofin tana zuga kad'an tarage yabata ruwa tasha Sannan yafara kiciniyar yimata wanka kuka sosai take inda Abunda ta tsana bai wuce ruwan sanyi ba shikuma bai Dora ba kasancewar kalanzir yak'are musu bai siyo ba dakyar yagama yanade ta a towel yaje toilet yazubadda ruwan yadawo ya wanke robar koda yadagata har ta soma bacci, baby oile dinta yad'auko yashafa mata yasa mata tufafi
Yafito da ita gindin iccen mangwaro da suke zama, hajiya maimuna ce tafito tareda k'aramun d'anta Kuma autanta mujaheed yadawo daga lesson yana rataye da jakar Shi, "malam bubakar ne sannu Ina wuni" ta gaida Shi " a' a hajiya maimuna barka da yau ya yara "
"Lafiya Lau ta bashi amsa " mujaheed yarussuna yagaida baban banuja yadafa kanshi "Allah yamaka albarka kaji "
"Amin Baba wannan Fatima ce yau da ita ake fira? Malam bubakar yace " Toh ya muka iya barinta ita kad'ai bashi yuwa "
"Hakane maimuna taba shi amsa muganta tasauya Ko har yanzu kyakkywa ce Zan komawa mujaheed" tareda kallon shi ta wutsiyar ido
Mujaheed yace "tab wannan tamun k'aramta dayawa yar primary five ce dai-dai Ni hajiya maimuna ta kalleshi tace "ja'irin yaro ay Fatima matar soja ce kamar yanda naji baban ta yace"
Malam bubakar yayi dariya yace "hakan ne fah banuja sai jarumi Wanda zai kwato mata hak'k'in uwarta" mujaheed yayi shiru yana kallon beautiful face d'in yarinyar, "momy Amma yarinyar tayi saurin Tara gashi dayawa " hajiya maimuna tayi dariya " haka nan uwarta take ko har ka manta mamanka hadizatu " mujaheed ya sosa k'eya "ay bazan mantaba Ina mata addu'a sosai "
Banuja tazille hannun momy tana k'ok'arin yi gurin mujaheed, hajiya maimuna tayi dariya tace " lallai yarinya tasan mijinta mujaheed sai ayi k'ok'ari a canza course, murmushi yayi yajuya da banuja yacewa baban ta semun dawo "
"Toh Allah kiyaye hanya" shago yaje da ita yazauna yana siya mata alewa da chocolate manya masu tsada seda yakusan kashe mata kud'in shi sannan yadawo gida da ita, kofar d'akin su yasame umar zaune rik'e da littafai yana dubawa " yafe sarkin boko " Umar ya watso masa mugun kallo ya maida kanshi k'asa yana cigaba da karatun Shi
Kuka ta soma yi lokacin momy na gurin wanka, mujaheed yatashi tsaye da ita yana jijjigata yana mata wasa, aikuwa kamar yakara zugata se kukan take ba k'ak'kautawa, Umar yaja wani dogon tsaki " wannan 'yar waye ka kwaso mana mai bak'in kuka haka"
mujaheed ya kalle banuja yace " 'yar gidan malam bubakar ce 'yar wajan margayiya hadiza"
umar Bai sake cewa komai ba dayaji kukan bamai k'arewa bane yatattara littafanshi yayi d'akin shi cike da haushin abunda yatashi daga gindin iccen gwaba Mai sanyi
Zamanshi keda wuya wayar shi ta soma ruri, tsaki yaja yajawo wayar yakashe ba ajima ba nokia Shi ta soma ring jiyayi kamar zai fasa wayar gashi se ring take , ring yak'are text yashigo zai Buda text d'in kenan calling yak'ara shigowa yadanna bottom call ďin tareda jan dogon tsaki,
Ajiyar zuciya tayi mai k'arfi haba sojana meyasa kake..... ya isa yabata amsa atak'aice bacci zanyi Zaki iya kira anjima that's all.....
Muje zuwa
www.abdulmkibab.hexat.com


Comments

Tadaga 5 from snovitrasuperpower is an oral medication for the management of erectile disorder or ED in males.

Buy Tadaga 5 mg Safely Online
Buy ED Pills Online at the Lowest Prices

Popular Posts